EFCC Na Neman Sarkin Gandun Zazzau Ruwa A Jallo


Daga Muhammad Farouk 


MADOGARA ta labarto cewa; Hukumar yaki da cin hanci da rashawa , EFCC na neman Sarkin Gandun Zazzau, Sama'ila Musa kuma shugaban kamfanin Dan-Arewa Integrated Services Limited Zaria, bisa zarginsa da zambo cikin aminci. 

EFCC sun zargi Sarkin Gandun Zazzau din bisa  karbar kudade bisa yaudara da damfara. 

EFCC din sun wallafa bayanan nemansa ruwa a jallo ne a takardar da suka wallafa a shafinsu na Facebook, wanda kakakin Hukumar, Wilson Uwujaren ya sanyawa hannu. Inda ya bayyana Sarkin Gandun Zazzau din a matsayin mutum mai shekaru 63 a duniya, kuma adireshinsa na karshe da aka sani shi ne gida mai lamba 20 Unguwan Sirdi dake cikin garin Zariya a jihar Kaduna. 


EFCC din sun nemi al'umma da su taimaka musu wajen nemansa, sannan duk wanda yake da bayanan yadda za a cafke shi zai iya tuntubar ofishin Hukumar dake garin Kaduna, Benin, Ibadan, Sakkwato, Gombe, Maiduguri, Makurdi, Ilorin, Inugu, Kano, Legas, Fatakwal da kuma Abuja. Ko kuma ya tuntubi lambobin wayarsu dake jikin Fostar kasan rahoton nan. 

Post a Comment

0 Comments