Farfesa Gwarzo Ya Yi Alhinin Rasuwar Dan Uwansa Naziru Gwarzo

 


Hukumar gudanar da Jami’ar Maryam Abacha (MAUN) sun mika sakon ta’aziyyarsu ga shugaban jami’ar kuma wanda ya assasa jami’ar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa rasuwar dan uwansa Naziru Yusuf Gwarzo.

Naziru ya rasu ne a daren ranar Lahadi 21ga watan Fabarairun 2021 a Sabon Layin Kara dake karamar Hukumar Gwarzo a jihar Kano. Inda ya rasu bayan rashin lafiya.

A sakon ta’aziyyar da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin a Kano, sun bayyan cewa Marigayin dan uwa ne ga Farfesa Gwarzo, wanda ya rasu a shekarun samartakansa. Inda aka gudanar da ta’aziyyarsa a gidansu dake Sabon Layi Gwarzo.

Hukumar gudanar da Jami’ar MAAUN din sun ce rasuwar Naziru babban rashi ne ba kawai ga ‘yan’uwansa ba harma da jihar Kano da Nijeriya baki daya.

 “kafin rasuwarsa, Naziru matashi ne da yake da karsashin ganin ci gaban matasa. Ya sadaukar da lokacinsa wajen taimakawa matasa ‘yan’uwansa domin su amfana da lokacinsu. Ya karfafe su wajen neman ilimin addini da na boko”, inji sanarwar.

Jami’ar ta MAAUN a karshe ta yi addu’ar Allah ya jikan Naziru ya yafe masa kurakuransa, ya kuma sanya shi a aljannah Firdaus.

Har wala yau dukkanin ma’aikatan Jami’ar Maryam Abacha American University sun mika sakon ta’aziyyarsu ga Farfesa Adamu Gwarzo da dukkanin iyalinsu bisa wannan babban rashi.

Post a Comment

0 Comments