Fulani Ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne -Sarkin Musulmi

 

Sarkin Musulmin Nijeriya, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa al'ummar Fulani "ba 'yan ta'adda ba ne".

Jaridar Daily Trust ta ruwaito sarkin na bayyana hakan ne a Abuja a ranar Laraba yayin da yake ziyara a hukumar aikin hajji ta ƙasa NAHCON.

"Na faɗa a baya kan haka cewa mu ba 'yan ta'adda ba ne ko miyagu," a cewarsa. "Tabbas akwai 'yan fashi daga cikinmu amma hakan ba zai sa a kira al'umma guda ko kuma Musulmai 'yan fashi ba."

Ya ƙara da cewa: "Ina alfaharin kasancewata Bafulatani kuma ko da a ce za a sake halittata bayan na mutu, wanda na san ba zai yiwu ba, zan roƙi Allah ya dawo da ni a matsayin Bafulatani.

"Ina alfaharin kasancewata Bafulatani amma ni ba ɗan ta'adda ba ne ko ɗan fashi."

Kazalika ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa za a gudanar da aikin hajji na 2021 saboda allurar rigakafin cutar korona da aka samu kuma ya shawarci Musulmai da su bi dokokin kariya daga cutar, waɗanda gwamnati ke sakawa kamar yadda rahoton BBC Hausa ya tabbatar.


 

Post a Comment

0 Comments