Garkuwa Da Dalibai A Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Yi Jawabi Ga Al'ummar Jihar


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Gwamna Bello Matawalle Maradun ya yi jawabi karon farko da sace dalibai mata na makarantar Sakandire dake Jangebe da ke cikin karamar hukumar Talatar Mafara a daren Juma'a da ta gabata.

Gwamna Matawalle Maradun ya bayyana kaduwarsa da jin labarin abin da ya faru ga daliban a daren Juma'a, inda ya ce;  tun daga lokacin suke ta fadi ta shi da jami'an tsaro don ganin yadda za a ceto wadannan dalibai ba tare da daya ta rasa ranta ba, inji gwamna Matawalle.

Kuma ya tabbatar da cewa, yanzu haka an kawo jiragen sama daga rundunar 'yan Sanda daga Abuja suna shawagi a cikin dajin domin ceto wadannan dalibai.

Gwamna Matawalle ya yi kira ga iyayan Daliban da su kara hakuri, gwamanti na iyaka kokarinta na ceto wadannan dalibai. Kuma ya yi kira ga al'ummar Jihar Zamfara da kasa baki daya da a taya su addu'a domi samun nasarar ceto daliban.

Post a Comment

0 Comments