Gobara Ta Hallaka Mutane Shida ‘Yan Gida Daya A Kano

 

Wata gobara da ta tashi a gidan wani mutum mai suna Abdurrahman Babawo ta hallaka mutane shida a Unguwar Na’ibawa ‘Yan lemo a karamar nukumar Kumbotso.

Kano Focus ta ruwaito gobarar da ta tashi cikin daren jiya Litinin da ake zargin maganin saurone ya sabbabata.

Shaidun ganin da ido sun ce gobarar da yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyar mai gidan da kuma yaransa biyu, da ‘yan uwansa biyu sai kuma ‘dan ‘dan uwansa da ya ziyarci gidan.

Haka zalika matar gidan da danta guda daya an garzaya da su asibiti domin basu kulawar gaggawa.

Tuni aka yi jana’izar wadanda suka rasun kamar yadda addinin musulunici ya tanada a unugwar ta Na’ibawa.

Sai dai da muka tuntubi hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ko kadan bata samu labarin tashi wutarba.

Post a Comment

0 Comments