Gwamna Ganduje Da Bagudu Sun Nufi Jihar Oyo Domin Tattauna Batun Makomar 'Yan Arewa A Jihar

 

Daga Hagu: Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano
Tare Da Gwamnan Jihar Birnin Kebbi, Atiku Bagudu

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da takwaransa na jihar Kebbi, Alhaji Atiku Abubakar Bagudu suna kan hanyarsu ta zuwa garin Ibadan dake jihar Oyo sakamakon matsalar rikicin kabilancin da ya barke a jihar tsakanin Yarbawa da Hausawa kamar yadda majiyarmu ta SAHELIAN TIMES ta labarto.

Gwamnonin biyu sun bar Kaduna ne suka nufi jihar Oyo a daidai lokacin da gwamnonin Arewa maso yamma da wadansu masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro ke taro a jihar Kaduna.

Majiyarmu ta ce duk da taron da ake yi a Kaduna a kan harkar tsaro ne, amma batun kashe-kashen da aka yi wa ‘yan arewa a jihar Oyo ba ya daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron. 

Daga cikin gwamnonin da suka samu halartar taron na Kaduna sun hada da gwamnan jihar Kano, Kaduna, Kebbi da Sakkwato, sai Sarakunan gargajiya da wadansu sauran masu ruwa da tsaki a Arewa. 

Taron dai ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Babagana Monguno ta shirya shi domin tattauna domin fito da hanyoyin da za su magance matsalar tsaro a arewacin Nijeriya.


Post a Comment

0 Comments