Gwamna Ganduje Zai Sanya Ranar Mukabala Da Shaikh Abduljabbar Kabara

 

A ranar Litinin ne ake sa ran za a mikawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje rahoton kwamitin da aka kafa da zai shirya mukabala tsakanin Malam Abduljabbar Kabara da sauran Malam jihar Kano.

Kwamishinan al’amuran addinai na jihar Kano dakta Tahar Adamu Baba Impossible ya sanar da hakan a yau Litinin.

Baba Impossible ya ce mutane basu fahinci sakon da aka fitar tun da fari ba, inda ya ce dama can gwamnati bata ce za a gudanar da mukabalar cikin makonni biyu masu zuwa ba.

Ya ce gwamnan Kano ya baiwa kwamitin da aka kafa ne mako biyu ya mika rahotonsa.

A cewarsa yanzu kuma kwamitin ya kammala aikinsa a yau Litinin, kuma zai mika rahoton ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Haka zalika ana sa ran da zarar Gandujen ya nazarci rahoton zai sanya ranar da za a zauna domin gudanar da mukabalar.

“Ai ba cewa aka yi a mako biyu za a yi mukabala ba, cewa akayi gwamnati ta ce a je a shirya cikin mako biyu a zomata da rahoto.

“Duk kwamitin da aka kafa sun kammala rahotonsu za kuma a mikawa mai girma gwamnan ranar Litinin.

“Bayan gwamna yayi studying din rahoto ya kammala zai sa ranar da za a yi.

“Amma su malamin a bangarensu shirinsu za su yi, ba shirin gwamnati ba ne.

“Amma shirin gwamnati kwamitoci sun zazzauna da wadanda za a gayyato daga wajen Kano an fadesu, da wadanda za a gayyato na ciki gida an gayyacesu, da jami’a tsaro da waye duk an gama an kammala.

“Yanzu sai mu saurari abinda gwamnati za ta ce, ita take da ikon sa rana, dama bata ce yau za a yi mukabalaba, ta ce ta bada mako biyu a shirya.

Game da kiraye-kirayen da wasu malamai ke yi na cewa bai kamaya a yi mukabalarba.

Babba Impossible ya ce ko kadan ba za su saurari korafin malaman ba, za su ci gaba da shirinsu na ganin anyi mukabalar.

Haka zalika ya ce malamai sun kawo karafin Abduljabbar, shi kuma ya nemi ayi masa adalci, don haka gwamnati za ta baiwa kowanne bangare hakkinsa.

Post a Comment

0 Comments