Gwamnati Na Biya Wa ‘Yan Nijeriya Naira Biliyan 50 Duk Wata Na Tallafin Wutar Lantarki –Minista Saleh Mamman

Ministan hasken lantarki, Injiniya Sale Mamman


Daga Muhammad Farouk

Ministan hasken lantarki, Injiniya Sale Mamman ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana bayar da tallafin wutar lantarki har na naira biliyan 50 a duk wata kamar yadda MADOGARA ta labarto. 

Wannan bayanin ya fito ne a cikin sanarwar da Aaron Artimas, mai taimakawa ministan kan hulda da kafafen watsa labarai ya fitar, inda ya ce ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin membobin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. 

A cewar ministan, ana bayar da wadannan kudaden ne ga kamfanuka masu raba wutar lantarkin saboda gazawar da suke yi wajen samar da kudaden wutar ga kamfanukan dake samar musu da hasken wutar lantarkin. 

 “bisa wannan, sakamakon karin kudi kadan da aka yi a bangaren wutar lantarkin, gwamnati ta rage tallafin da take bayarwa da rabin kudin, sai dai duk da hakan, fitar da kudin na shafar matsalar tattalin arzikin kasarnan,” inji ministan. 

Mamman ya bayyana damuwarsa bisa gazawar da kamfanukan da suke raba hasken wutar lantarkin ke nunawa wajen ayyukansu domin samar da kudaden da ya kamata domin taimakawa sauran bangarorin da suke da ruwa da tsaki a harkar samar da hasken wutar lantarki. 

Sale Mamman ya ce; “ya kamata ‘yan Nijeriya su sani cewa wadannan kamfanuka tuni suka zama na ‘yan kasuwa tun kafin zuwan wannan gwamnatin, sai dai gwamnati ba ta da wata damar da ya wuce ta ci gaba da lura da bangaren kafin a samar da mafita”, ya lurantar. 

Ya kara da cewa; “gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta shawo dukkanin matsalolin da ta gada wanda hakan ke kawo tsaiko ga nasarar bangaren wutar lantarkin”. 

Ministan ya ce mafin yawan kamfanukan da ke raba wutar lantarkin an siyar da su ga ‘yan kasuwa, inda suka maishe da abin kasuwanci a tsakaninsu, wanda ya ce wannan ya sanya lamarin ke da wahala wajen magance shi, sai dai ya ce duk da hakan gwamnati ba za ta zura ido ta bar lamarin haka ba. 

Minista Mamman har wala yau ya ce, a lokacin da wadannan matsalolin suka ki ci suka ki cinyewa, amma duk da haka gwamnatin tarayya ta samu nasarori masu yawan gaske, inda ya ce wanda ya hada da tabbatar da samar da hasken wutar lantarki fiye da da Megawatts 5,000, sabanin yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari suka same shi a kasa da Megawatts 4, 000. 

Dangane da samar da mita kuwa, Mamman ya yi bayanin cewa duk da hakkin masu raba hasken wutar lantarkin ne su samar da mita, amma ya ce gwamnatin tarayya ta shiga lamarin sakamakon koke-koken da al’umma suke yi bisa yadda ake tatsarsu kudi da yawan gaske. Inda ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da mita fiye da miliyan shida da za a raba kyauta ga ‘yan Nijeriya. Ya ce ya zuwa yanzu sun taba mita miliyan daya domin a fara raba shi, a yayin da sauran ake tsimayen jiransu. 

A karshe ministan ya yi kira ga DisCos da su yi hanzarin raba mitar kyauta ga wadanda ya kamata domin rage matsalolin da ake fama da shi. 


Post a Comment

0 Comments