Gwamnati Na Tattaunawa Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Dalibai Da Malamai A Jihar Neja

 

Makarantar GSC Kagara

Daga Muhammad Farouk 

Gwamnatin tarayya da na jihar Neja a halin yanzu na ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin da ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai da Malaman makarantar Sakandaren gwamnati dake Kagara a jihar Neja.

A daren ranar Talata ne ‘yan bindiga suka dira a makarantar ta kwana suka yi awon gaba da dalibai da Malamai da kuma wadansu mazauna kauyen.

Wani babban jami’in gwamnati ya bayyana cewa; an fara tattaunawa tsakanin gwamnati da masu garkuwa da jama’ar domin sasantawa a ‘yantar da daliban da Malaman.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an sanya wadansu shugabannin Fulani da wadansu ‘yan bindigar da suka tuba a baya wajen ganin sun shige gaba wajen sulhu domin ‘yantar da wadanda aka yi garkuwa da su. Rahotannin sun ce masu tattaunawar daga bangaren hukuma sun nemi taimakon ‘yan bindigar da suka tuba daga Zamfara da Katsina domin su shugabanci tattaunawar.

A jiya Laraba, gwamnatin jihar Neja ta ce ‘yan bindigar sun sace mutum 42 wanda ya hada dalibai 27 da kuma Malami uku sai mutanen kauyen 12 wanda ake zaton iyalin Malaman makarantar ne.

Har wala yau rahotanni sun ce a yayin da ‘yan bindigar suka dira makarantar, sun kashe dalibi daya da ya nemi guduwa, inda suka yi masa harbi uku.

Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya ce ba zai biya ko asi ba wajen ganin ya ‘yantar da wadanda ‘yan bindigar suka sace.


Post a Comment

0 Comments