‘Har Yanzu Ba A Tantance Adadin Daliban Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A GSC Kagara Ta Jihar Neja Ba’


 Har yanzu ba a tantance adadin daliban da ‘yan bindiga suka sace a yayin da suka afka wa makarantar Kwalejin kimiyya ta gwamnati (GSC Kagara) dake Kagara a jihar Neja ba. 

A Disambar bara, ‘yan bindiga sun sace daruruwan daliban makarantar Kankara dake jihar Katsina, lamarin da ya dagawa ‘yan kasa hankali, sai dai daga bisani an sake su bayan wadansu kwanaki. 

Rahotannin gani da ido, sun bayyana cewa; ‘yan bindigar sun isa GSC Kagara dake jihar Neja ne cikin kayan sojoji, inda suka dira a makarantar dake dauke da akalla dalibai dubu daya a daren ranar Talata. 

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta labarto cewa; ‘yan bindigar sun fi karfin jami’an tsaron da ke gadin makarantar, inda suka kwashe su suka nufi dazuka da su. 

Wasu bayanai sun nuna cewa wadansu daliban sun tsere bayan da ‘yan bindigar suka dira makarantar. Sai dai da safiyar yau Laraba, an kirga sauran daliban da suka rage domin tantance adadin da ‘yan bindigar suka sace. 

Sai dai majiyarmu ta PRNigeria ta ce hukumomin tsaro sun fara yunkurin tantance yanayin yankin, inda za su bibiyi inda ‘yan bindigar suka nufa, inda kuma aka ga jiragen sama na sojin sama na yawo a sararin samaniya domin gano inda aka nufa da daliban. 


Post a Comment

0 Comments