Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Hare-Hare Sun Hallaka 'Yan Najeriya Dubu Hudu Da 556 A 2020- Global Right

Wai Bincike da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Duniya da ake kira Global Rights ta gudanar ta bayyana yadda munanan hare-hare a sassan Nij...


Wai Bincike da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Duniya da ake kira Global Rights ta gudanar ta bayyana yadda munanan hare-hare a sassan Nijeriya ya hallaka mutum dubu hudu da dari biyar da Hamsinda shida cikin shekarar 2020 kawai.

Rahotan kungiyar da ya kunshi harin ta’addanci da fada tsakanin kabilu a yankunan kasar da kuma hare-hare, kisan gilla baya ga garkuwa da mutane, ya kuma nuna yadda aka samu karuwar mutanen da ke rasa rayukansu idan aka kwatanta da alkaluman shekarar 2019 da akalla mutum dubu 1 da 368.

Global Rights ta ce Nijeriya na ci gaba da fuskantar munanan hare-hare ta fuska biyu da suka shafi tsaro da suka hada da ayyukan ta’addanci da kuma na 'yan bindiga, baya ga wasu matsalolin da suka dabaibaye ta da suka hada da talauci da almubazzaranci da dukiyar kasa da rashin ayyukan yi, sai kuma illar da annobar korona ta haifar.

Kungiyar ta ce alkaluman da ta tattara sun nuna adadin rayukan da suka salwanta bara zuwa dubu 4 da 556, sabanin dubu 3 da 188 na shekarar 2019, kuma daga cikin wannan adadi dubu 3 da 858 fararen hula ne, yayin da 698 kuma jami’an tsaro ne.

Jihohin da suka fi fuskantar azabar kashe-kashen su ne Borno da mutane 1,176 sai Kaduna mai 628, Katsina mai 501, Zamfara 262 sannan Neja da 254 kamar yadda rahoton RFI Hausa ya tabbatar.


No comments