Hisbah Ta Kafa Kwamitin Binciken Babban Jami’inta Da Aka Kama A Otel Da Matar Aure A Kano

 

Sani Rimo

Hukumar Hisbah ta Kano ta kafa kwamitin bincike na mutum biyar da zai binciki zargin da ake yiwa jami’inta, Sani Rimo, bisa kama shi da ‘yan sanda suka yi da matar aure a wani Otel. 

Babban Kwamandan Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya tabbatar da batun kafa kwamitin, inda ya ce an bai wa kwamitin kwana uku ya kammala bincikensa. 

Karanta wannan labarin; ‘Yan Sanda Sun Cafke Babban Jam’in Hisbah Dake Kama Karuwai Da Matar Aure A Otel A Kano

 “Na kafa kwamitin bincike sannan na bai wa kwamitin kwana uku ya kammala bincikensa ya kawo rahoton binciken. Na kira dukkanin wadanda abin ya shafa domin a dauki bayanan kowa. Hisbah na da na ta dokokin, duk wanda aka kama ya karya dokar, zamu dauki tsattsauran mataki akan shi bisa dokokin da aka tanada,” ya tabbatar. 

Rimo dai ana zargin rundunar ‘yan sandar yankin Noman’s Land ne suka kama shi a Otel din Dingy dake Sabon Gari. Majiyar ‘yan sanda sun ce sun kama shi ne sakamakon bayanan da suka samu, inda suka je suka kama shi tare da matar aure a dakin Otel din. 

Rimo ya taba rike mukamin dake lura da kama Karuwai na Hisbah din. Kuma yanzu jami’i ne dake lura da kawo karshen bara a titunan jihar Kano na Hisbah din. 

Har yanzu dai ‘yan sanda ba su ce uffan ba kan lamarin a hukumance. Post a Comment

0 Comments