Iran Ta Sake Hada Sabon Rigakafin Cutar Korona

Kasar Iran da ta fi kowacce kasa a yankin Gabas ta tsakiya yawan wadanda cutar korona ta kashe, ta shirya gwajin sabon rigakafin cutar a karo na biyu. 

A karo na biyu kasar Iran ta fito da wani sabon maganin rigakafin cutar korona na cikin gida, kwana guda kafin kaddamar da aikin yi wa 'yan kasar allurar kandagarkin cutar. 

Hukumomi sun ce za a fara gwajin sabon maganin hadin kasar a jikin bil’adama cikin 'yan kwanakin da ke tafe. 

Massoud Soleimani, wani memba a kwamitin hada maganin rigakafin na Iran, shi ne shaida wa manema labaru hakan a garin Karaj da ke kusa da birnin Tehran. 

 Kamfanin harhada magungunan rigakafi na Razi da ke kasar ne dai ya hada sabon maganin.

Post a Comment

0 Comments