Iyayen Dalibai Mata Da Aka Sace A Jihar Zamfara Sun Yi Kukan Kura Sun Shiga Daji Neman 'Ya'yansu

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
 

Karanta labarin nan; YANZU-YANZU: 'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata A Zamfara

Karanta labarin nan; Yadda ‘Yan Bindiga Suka Dira A Makaranta Suka Sace Dalibai Mata A Jihar Zamfara


Iyaye da kuma shaidu sun ce ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan 400 daga makarantar sakandiren GGSS Jangeɓe a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da daddare.

Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.

Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata kusan 400 ne sakamakon kirga dukkan 'yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.

Har yanzu rundunar 'yan sandan jihar da ma gwamnatin Zamfara ba su ce komai a kan batun ba.

Kabiru sani, mataimakin shugaban Muryar Talaka ta jihar Zamfara, wanda aka sace 'ya'yan dan uwansa uku, ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun soma fasa kofar shiga makarantar sannan suka ci karfin mai gadinta kafin su sace daliban.

A cewarsa, barayin sun washi 'yan mata "sama da 374, 'yan matan kuma na jihohi ne daban-daban; akwai na Kaduna, Sakkwato, Kano, da Jigawa da Kebbi."

Ya ce yanzu haka sun shiga daji domin bin sahun 'yan bindigar.

Haka kuma wani mutum da aka sace 'yarsa daya mai suna Bilkisu da 'ya'yan 'yan uwansa biyu, ya ce daruruwan 'yan bindiga ne suka isa makarantar inda suka soma da kai hari kan masu gadi kafin su yi awon gaba da daliban.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin kubutar da daliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da yan bindiga suka sace a jihar Neja.

Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan fashin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

BBC na ci gaba da samun ƙarin bayani a kan wannan labari na Zamfara, za mu sanar da ku ci gaban da aka samu...

Post a Comment

0 Comments