Izala Ta Fi Fashi Da Makami Illa, Domin Makiya Manzon Allah Ne –Sakon Shaikh Dahiru Bauchi Ga Fulani

Shaikh Dahiru Usman Bauchi

Daga Muhammad Farouk 

Babban Shehin Darikar Tijjaniyyah, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya shawarci Fulani da ka da su kuskura su shiga kungiyar Izala bayan sun daina kidnafin, domin a cewar Shehin Malamin, kungiyar Izala makiya Manzon Allah (SAWW) ne, a don haka kin Annabi Muhammad kafirci ne.

Shehin Malamin yabayyana hakan ne a yayin hirarsa da ‘yan jarida kamar yadda MADOGARA ta sami cikakken Hirar, inda wakilinmu ya nakalto mana cikakkiyar hirar kamar haka:

Shehin Malamin ya fara da cewa; “don Allah don Annabi Fulani, ku rufa mana asiri, kun bata mana suna, ga shi ana korar mu ko’ina kamar mu ba ‘yan kasa ba. Subhanallah. Ku bar wannan mugun hali. Masu mugun halin nan duk sunansu, sunansu ba ya fitowa sai sunanku. Saboda ba ku gaji abin da kuke yi ba. Komin kankantarku a cikin  mutanen sunanku za a ji saboda ba ku gada ba. Saboda haka don Allah ku rufa mana asiri mu Fulani, ku gyara mana sunayenmu. Maimaikon ku ci gaba da bata sunan Fulani; kune ‘yan fashi da makami, kune ‘yan fashin daji, kune Kidnafin, mune masu miyagun ayyuka, duk abin da bamu gada ba. Allah ya kiyaye mu, ya kiyaye mana addininmu”.

Ya ci gaba da cewa; “ina jawo hankali musamman na Fulani din, kar kuma su sake shiga wani abu wanda yake kusa da kidnafin din. Ina ji musu tsoro ka da ku shiga Izala kuma. Kar ‘yan Izala su dauke su kuma su ce za su yi musu wani abu bayan suna ‘yan fashi, suna ‘yan kidnafin su zama ‘yan Izala. Wato sun bar addini ke nan su zama makiya Annabi Muhammadu (SAW). Abin da ya sa ake kin Izala, ba ta ganin darajar Annabi Muhammadu (SAW). Rashin ganin darajar Annabi Muhammadu din nan idan aka fada shi, abin da aka fada ya fi ma kila fashi din muni. Domin fashi zaluntar mutane ne, amma kin Annabi Muhammad (SAW) fita daga addini ne. Ku kiyaye kanku kar ku sake ku shiga Izala. Kar ku yarda ku rika fashi da makami, kar ku yarda ku yi kidnafin. Duk wadannan miyagun abubuwa ne”.

Ya kara da cewa; “ku nemi mutanen da ba wannan suke yi, ku hada kai da su. Kar ku yarda wadanda suka sace muku shanu, su dawo su sace ku, su je su bata muku hali, su bata muku tunani, su koya muku fashi, su koya muku bindiga, su koya muku kashe-kashen mutane, su koya muku miyagun halaye. Allah ya kiyaye mu, Allah ya kiyaye danginmu Fulani. Allah ya kiyaye mana jama’armu Musulmi gaba daya”, inji shi.

Ya karkare da cewa; “kuma zan nanata, ka da ku fito cikin wadannan abubuwan kuma ku fada Izala, kun fada Izala shi ke nan kun fada cikin abin da ya fi wannan muni. Da kuna cikin tabo kun fita kun fada cikin kashi ke nan. Ina muku fada Fulani ka da ku shiga Izala. Izala ba halinku bane. Shi Bafullatani duk yadda ka yi ba za ka raba shi da Annabi Muhammadu ba, duk yadda ka yi. Miskini sai ka ga ba ya sallah, bai san mene ne addinin ba, amma tunda ya gada shi Musulmi ne, sai ka ji yana Annabijo-Annabijo, za ka ji Annabijo-Annabijo, shi ba za ka raba da Annabi Muhammadu ba. Idan ya fita cikin wannan fashi da makami, kun fada Izala, to kun fada cikin abin da ya shiga cikin fashi da makami din. Don fashi da makami zambo ne, zalunci ne, amma kin Annabi Kafirci ne! Allah ya kiyaye mu!”

Post a Comment

0 Comments