Jami'an 'Yan Sanda Sun Sake Cafke Mahdi Shehu


Jami'an 'yan Sandan Nijeriya sun yi nasarar sake cafke Mahdi Shehu a tashar jirgin kasa ta Kubwa dake birnin Tarayya Abuja kamar yadda Taskar Labarai ta labarto. 

Mahdi an kama shi ne da yammacin yau bisa alaka da wani bincike da ake yi a kansa bisa zargin da gwamnatin Katsina ke yi masa na yunkurin bata wa gwamnatin suna. 

Taskar Labarai ta labarto cewa; Mahdi Shehu za a dawo da shi Katsina ne domin gurfanar da shi gaban babbar kotun Katsina domin ya amsa tuhumar da ake yi masa. 

Post a Comment

0 Comments