Jami’ar MAAUN Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hakimin Kabo, Alhaji Abba Ahmad

Marigayi Alhaji Abba Ahmad
 

Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) dake Kano ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan Alhaji Abba Ahmad, Ma'aji na Watari kuma Hakimin Kabo dake jihar Kano bisa rasuwa da ya yi a ranar Juma’ar 19 ga watan Fabarairun 2021.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya assasa Jami’ar shi ne ya mika sakon ta’aziyyar a  sanarwar da ya sanyawa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Kano a ranar Juma’a.

Marigayin ya rasu yana da shekara 78 a asibiti a Kano, inda ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya sha biyu, da jikoki da dama.

Farfesa Gwarzo ya bayyana Marigayi Ma’ajin Watari a matsayin daya daga cikin jigon Jami’ar MAAUN, wanda ya taimaka matuka gaya tun farkon yunkurin kafa jami’ar ta hanyar bayar da shawarwari, wanda ya ce duk da ga shi Allah bai kaddara zai ga Jami’ar ta fara aiki ba.

“muna addu’ar Allah ya yafe masa dukkanin kurakurensa ya kuma ba shi aljannah Firdaus,” inji Farfesa Gwarzo.

Abubakar Gwarzo ya bayyana rasuwar mai sarautar gargajiyar a matsayin wani babban rashi da aka yi, ba kawai ga iyalinsa ba, harma ga al’ummar jihar Kano baki daya. Ya ce musamman idan aka yi duba da irin gudummawar da ya bayar wajen taimakon marasa galihu a cikin al’umma a lokacin da yake raye.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya bai wa iyalinsa da ‘yan’uwa da abokan arziki hakurin jure rashin da suka yi.

Tuni aka bizne marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Kano, inda bayan bizne shi aka gudanar da addu’o’i a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Post a Comment

0 Comments