Jami’in FRSC Ya Mayar Da Naira Dubu 420 Ga Iyalin Da Hatsari Ya Rutsa

Daga Muhammad Farouk

Wani jami’in Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, FRSC ya mayar da naira dubu dari hudu da ashirin da ya tsinta a inda wani hatsari ya auku a daidai Akinfosile dake titin Legas zuwa Ore a karamar hukumar Okitipupa ta jihar Ondo. Inda ya maishe da kudin zuwa ga iyalin wanda hatsarin ya rutsa da shi. 

Olusegun Aladenika, Kwamandan FRSC a Ore, shi ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan a ranar Lahadi a Ore. 

Aladenika ya ce kudin na wani mai suna Nnamdi Okoro ne wanda ya rasu sakamakon hatsarin, inda aka mayar da kudin ga iyalinsa wanda aka bai wa wani mai suna Chidiebere Nnewe, bayan ya rubuta cikakken bayanansa da kuma rantsuwa a ofishin ‘yan sandan Nijeriya dake Omotosho a kuma gaban jami’an Kungiyar NURTW reshen Igbotako.

Kwamandan FRSC din ya ce hatsarin ya auku ne tsakanin wata motar Toyota Picnic mai dauke da lamba BEN 417 CV da kuma wata farar Lexus mai lamba RX 350 SUV a ranar 18 ga watan Fabarairu da misalin karfe 8:30 na safe a Akinfosile. 

Inda ya tabbatar da cewa Direban motar Toyota Picnic da kuma fasinjan dake ciki nan take suka mutu. 

Kwamandan FRSC din ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon gudu na wuce misali, inda ya shawarci direbobi da su rika kiyaye ka’idojin tuki a babban hanya domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma. 


Post a Comment

0 Comments