Kakakin Ganduje Salihu Tanko Yakasai Ya Bace 6at

Daga hagu: Salihu Tanko Yakasai Da Gwamna Ganduje
 

Rahotannin da ke shigowa MADOGARA na nuni da cewa; mataimaki na musamman kan kafafen yaɗa labarai, Salihu Tanko Yakasai ga gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bace bat tsawon awa 25 babu labarinsa. 

Wani mai suna Injiniya Abba shi ne ya wallafa hakan cikin harshen Turanci a shafinsa na Twitter a daren jiya Juma’a da misalin karfe 9 da minti 22 na dare. 

Injiniya Abba ya wallafa cewa: “iyalai, abokai da kuma ‘yan’uwa har zuwa yanzu sun kasa sanin inda @dawisu yake har na tsawon awa 14. Dukkanin layukan wayansa ba a samunsa tun bayan barin gida da ya yi da misalin karfe 4 na yammacin jiya. Idan kuna da wani bayani dangane da inda yake, ku taimaka ku sanar damu. Wannan sakon gaggawa ne! Mungode.” Ya rubuta. 

Tsaka da hada rahoton nan, bayanai suka tabbatar da cewa; Dawisu yana ofishin hukumar tsaro ta DSS, sai dai ba a tantance ko na wani jiha ko gari ba. 

Idan ba ku manta ba, Salihu Tanko Yakasai, wanda hadimin gwamnan Kano ne Dr Abdullahi Umar Ganduje kan kafofin yada labarai, ya ce gwamnatin APC ta gaza a wajen kare 'yan Nijeriya.

Yakasai ya wallafa hakan ne a shafinsa na twitter a ranar Juma'a, a yayin da yake maida martani ga labarin sace dalibai mata na GGSS Jangebe a jihar Zamfara da 'yan bindiga suka yi.

Ba nan ya tsaya ba, Salihu Tanko Yakasai da aka fi sani da Dawisu a shafin Twitter, ya rika ‘retweeting’ labarai da ra’ayoyin al’umma kan sace daliban wanda ba za su yi wa gwamnati dadi ba. 

Salihu Tanko Yakasai da mahaifinsa Tanko Yakasai

Karanta labarin nan; Satar Dalibai: Gwamnatin APC ta gaza -Hadimin Ganduje

Post a Comment

0 Comments