Kashe-Kashen Hausawa A Oyo: Masu Ta'ammuli Da Soshiyal Midiya Sun Fara Dawo Da ‘Yan Arewa Gida

Wata kungiyar Arewa masu ta’ammuli da shafukan sada zumunta sun yi wani yunkuri na fara dawo da ‘yan Arewa gida daga jihar Oyo, hakan ya faru ne sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a jihar. 

Majiyarmu ta Jaridar SAHELIAN TIMES ta zanta da daya daga cikin wadanda suka yi wannan yunkurin na dawo da ‘yan Arewar gida, inda ya tabbatar musu da cewa; zuwa yanzu motocin Bas na Toyota guda hudu ne suka fara kwaso ‘yan Arewar da suke rasa muhallansu daga jihar Oyo zuwa jihohinsu na Arewa. 

Majiyar tamu ta ci gaba da cewa; dubban ‘yan arewa ne aka raba su da muhallansu, inda suka tare a fadar Sarkin Shasha bayan barnar da aka tafka a kasuwar ta Shasha dake karamar hukumar Akinyele dake jihar Oyo a karshen makon nan da ya gabata. 

“wannan yana daga cikin irin gudummawar da zamu iya bayarwa a matsayinmu na masu ta’ammuli da shafukan sada zumunta. Ba za mu zauna mu kasa tabuka komai ba a daidai lokacin da ake kashe mana ‘yan’uwa”, inji su. 

Ya karkare da cewa; “babban kalubalenmu shi ne bamu san me ka iya faruwa a hanyarsu ta dawowa ba, domin hukumomi sun ki yin komai wajen magance matsalar”, ya tabbatar. 


Post a Comment

0 Comments