KORONA: Afirka Ta Bukaci Karin Dala Biliyan 500 Daga IMF

 

Daga Muhammad Farouk 

Kasashen Afirka sun bukaci karin Dala biliyan 500 daga Hukumar Bada lamuni ta duniya (IMF) da kuma jinkirta karbar bashin da ake bin su domin shawo kan matsalolin da annobar korona ta haifar musu.

An gabatar da wannan bukatar ce lokacin da ministocin kudade daga nahiyar Afirka suka gudanar da taro a karkashin Hukumar Tattalin Arzikin Kasashen nahiyar da kuma Hukumar Bada Lamuni ta duniya kamar yadda RFI Hausa ta labarto.

Hukumar bada lamunin ta ce asusun da kasashen Afirka ke bukatar ba su wadannan kudade har Dala biliyan 500 an kirkire shi ne a shekarar 1969 domin tallafawa asusun ajiyar kasashen dake cikin Hukumar.

Ya zuwa yanzu an baiwa kasashen Dala biliyan 281 domin tunkarar matsalolin da suka addabe su.

Shima bankin Duniya ya bukaci kasashen dake cikin kungiyar G20 da su taimakawa kasashen masu tasowa wajen amfani da kudaden wajen fuskantar kalubalen da annobar korona ta haifar domin kare lafiyar jama’ar su.

Ya zuwa yanzu kasashen Duniya 73 suka cancanci daga musu kafa wajen jinkirta karbar bashin da ake abin su saboda matsalar da annobar ta haifar.

Post a Comment

0 Comments