Korona Na Ci Gaba Da Sauki A Nijeriya


 Hukumar NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 542 da suka kamu da annobar korona a ƙasar a ranar Litinin. Lamarin da ya sanya kwana hudu ke nan a jere cutar na kara sauki sakamakon yadda ake samun kasa da mutum 700 da ke kamuwa da cutar sabanin watannin baya da ake samun kusan mutum dubu biyu da cutar ke kamawa a rana daya. 

Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 99 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 91 a jihar Kwara da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

Ebonyi na da mutum 48 da suka kamu da cutar a wannan rana. Ogun na da mutum 44 sai Kaduna mai mutum 42.

A jihar Oyo an samu mutum 33, yayin da ƙarin mutum 25 suka kamu a Ondo, sai mutum 24 a Abuja, babban birnin ƙasar, Kebbi kuma na da 23.

Post a Comment

0 Comments