Kotu Ja Kunnen Kakakin ’Yan Sandan Kano Tare Da Cin Tararsa Naira Miliyan Daya

 

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa

Daga Wakilinmu

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta ci tarar kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa Naira miliyan daya saboda take hakkin bil’adama.

Kotun ta ci tarar tasa ne kan tsare wani mai hulda da kafafen sada zumunta, Bashir Bashir Galadanci bisa zargin Kiyawan da bata masa suna a shafukan sada zumunta.

A bara ne dai jami’an ’yan sandan suka cafke Bashir Galadanci bisa zarginsa da yabon tsohon kakakin rundunar a jihar, Magaji Musa Majiya da kuma caccakar Kiyawan a mafi yawan rubuce-rubucen da yake yi a kafafen.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Obira ya ci tarar Kiyawa Naira miliyan daya saboda take hakkin Bashir din na sama da sa’o’i 48.

Kotun ta kuma ce hakan ya saba da ’yancin da yake da shi na fadin albarkacin bakinsa kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bashi.

Kazalika, kotun ta ce bai kamata a kama Bashir din ba, ko kuma a sake gayyatarsa ofishin ’yan sanda a kan lamarin, tare da umartar Kakakin da ya nemi gafararsa ta gidajen rediyo.

Sauran wadanda ake kara a shari’ar sun hada da Insifekta Abba Jakara, direban Kakakin, tsohon jami’in dake kula da Sashen Yaki da ’Yan Daba na rundunar da kuma Sufuritandan ’yan sanda, Uba Bangajiya.

Post a Comment

0 Comments