Ku Daina Kabilantar Da Ta’addanci –Shugaba Buhari Ya Yi Gargadi

Shugaba Muhammadu Buhari

Daga Muhammad Farouk

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadi akan a daina kabilantar da ta’addanci, inda ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa zai ci gaba da maganin ‘yan ta’adda, masu garkuwa da jama’a da kuma ‘yan bindiga da sauran bata gari wadanda suka zama barazana ga ‘yan kasa. 

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin zaman da ya gudana a Kaduna tare da gwamnoni 19 na Arewacin Nijeriya, da sauran shugabannin yankin, da Sarakunan gargajiya, inda ya jaddada cewa; “’yan ta’adda sunansu ‘yan ta’adda, kuma a hakan ya kamata a yi maganinsu ba tare da an kabilantar da su ba”. 

Rahotanni sun bayyana cewa zaman ya gudana ne a Kaduna a wani mataki na magance matsalar tsaro da kuma tattalin arziki da ake fama da shi a yankin. 

Wadanda suka samu damar halartar zaman sun hada da; dukkanin ‘yan majalisar dake wakiltar yankin a matakin Tarayya, Shugaban hukumar tsaro ta DSS, Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da kuma wakilan kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), da kuma shugabannin kungiyar Dattawan Arewa (NEF). 

Shugaba Buhari, wanda shugaban ma’aikatar fadar gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari ya wakilta, ya ce gwamnatinsa za ta fuskanci dukkanin kalubalen matsalar tsaro da take fuskanta, sannan za ta tabbata da ta tsamar da ‘yan Nijeriya daga matsalar talauci da durkushewar tattalin arziki. 

“gwamnati za ta ci gaba da magance matsalar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a da sauran bata gari wadanda suka zama barazana ga ‘yan kasa a fadin kasarnan”, shugaban kasar ya tabbatar. Inda ya kara da cewa sabbin Hafsohin tsaro tuni ya dora musu alhakin fito da sabbin dabaru da zai kawo karshen wannan matsalar ta tsaro da ake fuskanta wanda rayukan ‘yan Nijeriya ke cikin barazana. 


Post a Comment

0 Comments