Ku Daina Karya, Ni Ba Ni Da Wata Gona -Raddin Shekau Ga Sojoji

Daga Muhammad Farouk

Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, da aka fi sani da Boko Haram bangaren Abubakar Shekau ya dauki alhakin harin da aka kai a garin Maiduguri dake jihar Borno a ranar Talata da rokoki. 


A cikin wani sabon bidiyo na minti biyar da da dakikoki 32 da ya saki a ranar Alhamis, shugaban Boko Haram din, ya ce wata runduna ce ta Boko Haram din ta kai hari. 

Shekau har wala yau ya nesanta kansa da wata gona da aka ce ta shi ce wanda sojojin Nijeriya suka kona ta. 

Karanta labarin nan; Sojojin Nijeriya Sun ‘Ƙwace Gonar Shekau’ A Dajin Sambisa

Bidiyon ya nuna wadansu ‘yan ta’addan dauke da bindigar AK suka shiga garin na Maiduguri suka kaddamar da hari. Sannan sun nuna wani ‘machine gun’ a yayin harin. 

‘Yan ta’adda da dama ne ke da hannu wajen kaddamar da hare-haren a birnin na Maiduguri. Bidiyon ya nuna yadda ‘yan Boko Haram din suka harba rokoki cikin birnin, kafin daga bisani ya nuna yadda suka kuma bude wuta da makamansu. 

Majiyarmu ta HumAngle ta labarto cewa an kai harin ta yankin Kaleri, wani kauye kusa da Jami’ar Maiduguri da yammacin ranar Talata. 

Harin na rokoki ya kashe akalla mutum 15, tare da raunata fiye da mutum 40 a wurare daban-daban. 

Wannan shi ne hari irinsa na farko a cikin shekaru masu yawa, inda ‘yan ta’adda suka zo birni da kansu da rana suka kaddamar da hari. A baya sun yunkuri daban-daban domin kaddamar da harin, sai dai a karshe harin na karewa a wajen garin Maiduguri. 

Sojojin Nijeriya suna aiki tukuru wajen yaki da Boko Haram da kuma bangaren da suka balle daga ISWAP, a arewa maso gabashin Nijeriya da kuma Lake Chad, kamar yadda yadda Hukumar hulda da kasashen waje ta tabbatar, inda suka kara da cewa ta’addancin na Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutum 37, 500 tun 2011 tare da sanya mutum miliyan 2.5 gudun hijira a yankin. 


Post a Comment

0 Comments