Ku Tanadi Makamanku A Zaben 2023 –Sakon Shugaban APC Na Kano Ga Magoya Baya

 

Daga Muhammad Farouk

Mukaddashin shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya shawarci dukkanin magoya bayan jam’iyyar a jihar da su tanadi makamansu domin maganin ‘yan adawa a ranar zabe da za a gudanar a shekarar 2023. 

Wakilin MADOGARA ya labarto mana cewa; shugaban APC din ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi ga dimbin magoya bayan jam’iyyar a Kano a yayin kaddamar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar da ya gudana a ranar Juma’a. 

Bayan shewa da daddaga makamai da magoya bayan APC din suna kuma taken APC din, mukaddashin shugaban jam’iyyar na jihar, ya nemi da su sauke makamansu, inda ya ce; “zamu fada muku lokacin da za ku yi amfani da su. Idan kuka samu duk wani dan adawa na yunkurin aringizon zabe, kar ku kyale shi, ku gama da shi nan take, ba kuma abin da zai faru”, inji Alhaji Abdullahi Abbas. 

Ya ci gaba da cewa; “wannan shi ne hukuncina. Shi ne kuma hukuncin duk wani da ya yi yunkurin aringizon zabe. Ba abin da zai faru,” Abdullahi Abbas ya tabbatar. 

A na shi jawabin, gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya nemi dukkanin sabbin shugabannin kananan hukumomin 44 da kansiloli 484 da za su gudanar da ayyukan kamar yadda aka yi hasashe daga gare su. 

Ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa da wadansu ayyukan almundaha, inda ya ce daga cikin manufofin gwamnatinsa akwai yaki da rashawa. 

An dai shaidi mukaddashin shugaban APC din na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, da shahara wajen yin jawabai kan ‘yan adawa da ka iya kawo tashin hankali. 

Post a Comment

0 Comments