Kwamitin da aka kafa domin tabbatar da sabuwar Jami’ar ‘Franco-British International (FBI) University’ dake Kaduna ta ayyana Dr Abdullahi Abubakar Kankia a matsayin Sakataren tsare-tsare da tabbatar da kafuwar Jami’ar (PIC).
Hakan na dauke ne a cikin takardar ba shi mukamin da jagoran ganin an kafa Jami’ar ta FBI, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu, wanda kuma aka rabawa manema labarai a Kano a yau Alhamis.
A cewar takardar, mukamin na shi zai fara aiki ne a nan take, kuma an ba shi mukamin ne sakamakon zaman da kwamitin na PCI ya yi kan ganin an kafa Jami’ar ta FBI a Kaduna a ranar Larabar 24 ga watan Fabarairun 2021.
Takardar ta bayyana cewa; “muna farin cikin sanar da kai cewa an nada ka mukamin Sakataren tsare-tsare da tabbatarwa na kwamitin Jami’ar”.
Takardar ta ci gaba da cewa; “kwamitin na da imanin cewa zaka yi amfani da kwarewarka wajen ganin aikin kafa jami’ar ya yiwu”.
0 Comments