Lauyoyin Shaikh Abduljabbar Sun Janye Karar Da Suka Shigar Da Gwamnatin Ganduje

 

Daga Hagu: Shaikh Abduljabbar Da Gwamna Ganduje

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta amince da janye karar da Lauyoyin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara suka yi kan neman hakkinsa da gwamnatin jihar Kano karkashin Dr Abdullahi Ganduje suka take masa na kulle masallacinsa da hana shi gabatar da wa’azi tare da yi masa daurin talala. 

Karar da Lauyoyin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara suka shigar gabanta sun nemi kotun ta umurci gwamnatin Kano ta cire ɗurin talalar da take yi masa. Sai dai dama tun a jiya Laraba 17 ga watan Fabarairun 2021, Shehin Malamin ya roki Lauyoyinsa a wani sabon bidiyo da ya yi akan su janye karar da suka yi wa gwamnatin ta Kano. 

Mai Shari'a Lewis Alagoa ya kori ƙarar ce bayan da lauyan Abduljabbar, Rabi'u Shu'aibu Abdullahi, ya gabatar da buƙatar mai ƙarar ta janye ƙorafin na su daga gaban kotun.

Lauyoyin da ke kare gwamnati ba su yi wata-wata ba suka amince da buƙatar kuma nan take mai shari'a ya kore ta.

A ranar Alhamis da ta gabata ne lauyoyin Shehin Malamin suka shigar da ƙara da nufin neman kotu ta tilasta wa gwamnati da Kwamishinan 'yan sanda da shugaban tsaro na hukumar DSS a Kano da su janye jami'an su da suka girke a kofar makarantarsa da gidansa a Unguwar Filin Mushe.

Gwamnatin Kano na tsare da Malamin ne a gidansa biyo bayan zarginsa da "kalaman tayar da fitina" game da lamuran Musulunci a farkon watan Fabarairu da wadansu Malaman da ba sa fahimta da shi suka kai korafinsa gaban gwamnati.

Malamin ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa, sannan ya buƙaci a haɗa muƙabala tsakaninsa da sauran Malamai a jihar, buƙatar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince kuma ya ce gwamnati za ta saka rana da wurin da za a gudanar da ita.


Post a Comment

1 Comments

  1. Wannan shine adalchi wajan isar da saqo ba kamar bbc na

    ReplyDelete