Masarautar Gwandu Ta Dakatar Da Wazirinta, Alhaji Abdullahi Umar


Daga Wakilinmu


Masarautar Gwandu dake jihar Kebbi a karkashin Sarki Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar CFR, mni ta dakatar da wazirin masarautar, Alhaji Abdullahi Umar. 

Dakatar da Wazirin ya biyo bayan matakin da Sarkin ya dauka bisa wadansu wasiku guda uku da Wazirin ya rubuta zuwa ga Sakataren masarautar a ranar 9 ga watan Fabarairun 2021, da kuma wacce ya rubuta duk a wannan rana ga Usman Dalhatu Zaria ta ofishin Sakataren masarautar da wadansu wasikun da Wazirin ya rubuta ga wadanda ya sani kawai. 

Sanarwar dakatar da Wazirin ta fito ne a cikin wata takarda da MADOGARA ta samu kwafinta, wanda Magatakardar masarautar, Alhaji Musa Usman Bashar ya sanyawa hannu a ranar 23 ga watan Fabarairun 2021.

Takardar ta ce dakatarwar zai fara aiki daga ranar 23 ga watan Fabarairun 2021 har zuwa kuma wani lokacin. 

Ga kwafin takardar a kasa: 

Post a Comment

0 Comments