Mun Goyi Bayan Shirya Mukabala Da Shaikh Abduljabbar –Kungiyar CIPEP

 

Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Daga Muhammad Farouk

An yaba wa gwamnatin jihar Kano da ta dauki matakin shirya mukabala a tsakanin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da hadakar wasu Malamai a jihar dake zarginsa da cin zarafin Annabi da Sahabbai.

Wata kungiya mai suna Citizens For Peace and Progress (CIPEP), ta bayyana farin cikinta a cikin wata takardar sanarwa da jami’inta na yada labarai, Abdullahi Alhassan ya sanya wa hannu, tana maraba da yadda aka yi amfani da tunani da kuma bin doka da oda ya dawo a jihar Kano.

A wani sashe na takardar sanarwar tana cewa; “Biyo bayan tashin-tashinar da aka samu a jihar Kano saboda haramta wa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara yin wa’azi a jihar da gwamnati ta yi da kuma sauyin tunani ya zuwa shirya tattaunawa, mu ‘yan kungiyar Citizens For Peace and Progress (CIPEP) na sanar da amincewarmu da matakin komawa ga amfani da tunani da kuma bin doka da oda da gwamnatin jihar ta yi”, inji sanarwar.

Ya kara da cewa; “jamar’ar jihar Kano za su shaida cewa Malamin da ake tsangwama na gudanar da harkokinsa, tare da kula da zaman lafiya wanda wasu Malamai ba su aminta da irin tasa fahimtar ba game da Hadidai, inda suka zarge shi da cin zarafin Annabi (S) da Sahabbansa”.

Ya ci gaba da cewa; “Gwamnatin jihar Kano ta kasance ba ta da zabi da ya wuce ta dirar wa Shaikh Abduljabbar bayan hadakar Malamai sun zuga ta don gudun ka da Malaman su tunzura jama’a zuwa ga tashin hankali a jihar in gwamnati ba ta ba su goyon baya ba. Haka kuma, jama’ar jihar Kano shaidu ne cewa Malamin da ake tsangwama, bisa tabbacin da yake da shi a kan fahimtarsa game da Hadisan Annabi (S), ya sha kira ga Malaman su zo a yi mukabala domin tabbatar da gaskiya a tsakaninsu”, inji kungiyar.

Sai dai kungiyar kuma ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta tabbatar an gudanar da mukabalar bisa wasu shawarwari da ta bayar domin gujewa tashin hankali da warware matsalar.

Ta ce; “duk Malaman da suka yi hadaka wurin tsangwamar Shaikh Abduljabbar akan fahimtarsa dole su halarta. Domin al’umma su tabbatar da adalcin gwamnati da rashin nuna goyon bayan wani bangare a wannan mataki da ta dauka. Duk Malaman da abin ya shafa dole su zo da kan su ka da kowa ya turo wani wakili”.

“yada zaman ga al’umma ta hanyan amfani da rediyo da gwamnati ta ambata za ta yi, ya dace kwarai, kuma kada ta fasa. Wannan mukabala ya kamata ta jawo bangarorin biyu zuwa ga fahimtar juna da kuma girmamawa, ba wai za a yi ta ne domin samun wanda ya yi nasara, ko wanda aka kayar ba. Ya kamata ya zama za a yi ta ne domin al’umma su ji bambance-bambancen da ke tsakanin fahimtar Malamai, sai su yi wa kansu hukunci. Idan kuma hadakar Malaman da ke neman a hana Shaikh Abduljabbar wa’azi suka ki yarda su halarci wannan mukabala, dole kuma gwamnati ta kyale shi ya ci gaba da harkokinsa yadda ya saba ba tare da wata tsangwama daga gare su ba,” kamar yadda  kungiyar ta fada a takardar sanarwar.

Daga karshe kungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta tabbata ta bi wadannan shawarwari domin kare mutuncinta a idon al’umma da gujewa zargin ta da goyon bayan wani bangare. Ta ce ta hanyar haka ne kawai za ta iya nuna gaskiya da adalci.

Post a Comment

0 Comments