Mun Kawar Da Talauci Baki Daya A China -Xi Jinping

Shugaban China, Xi Jiping
 

Shugaban Kasar China, Xi Jinping ya ce kasarsa ta fatattaki talauci gaba daya. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani biki na musamman domin murnar kawo karshen talaucin a birnin Beijing wanda ya gudana a ranar Alhamis, ya kuma jaddada cewa hakan wani babban lamari ne mai cike da tarihi, sannan nasara ce babba.

A watan Nuwambar 2013 ne dai shugaban ya sha alwashin cewa jam’iyyar Kwaminisanci ta kasar za ta kawo karshen talaucin a China.

Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane miliyan 10 ne aka rika tsamowa daga matsanancin talaucin a kowacce shakara tun shekarar 2012, lamarin da ya zuwa yanzu ya kai ga tsamo mutane miliyan 98.99 musamman a yankunan karkara.

Bugu da kari, Shugaba Xi ya ce sama da jimlar mutane miliyan 770 ne yanzu suka fita daga kangin na talauci a kasar cikin shekaru 40 da suka gabata.

Shugaban ya ce sun sami gagarumar nasarar ne cikin shekaru takwas din da suka gabata ta hanyar zuba zunzurutun kudade kimanin Yuan tiriliyan 1.6 (kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 246) a bangaren shriye-shiryen yaki da talauci.

Post a Comment

0 Comments