Ngozi Okonjo-Iweala Ta Zama Mace Ta Farko Kuma 'Yar Afrika Da Za Ta Rike Shugabancin WTO

 

Bayan shafe kimanin watanni shida ba tare da shugaba ba, yau Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO ta nada tsohuwar Ministar Kudi ta Nijeriya a matsayin shugabarta mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko.

Ngozi Okonjo-Iweala ta maya gurbin dan Brazil Alberto Azevedo wanda ya sauka daga mukamin a watan Augustan bara, gabanin cikar wa’adin mulkinsa.

Bisa tsari dai, sai duka kasashe 164 mambobin kungiyar sun amince kafin nada shugaba – don haka lokacin da Amurka karkashin shugabancin Donald Trump ta ƙi amincewa da nada Ngozi Okonjo-Iweala aka shiga kiki-kaka, har sai da shugaba Joe Biden ya hau karagar mulki a watan Janairu, kana ya sauya matsayin na gwamnatin Trump.

Post a Comment

0 Comments