Nijeriya Ta Sayi Allurar Riga-kafin Korona Fiye Da Miliyan Daya

 

A Nijeriya cutar korona ta yi ajalin mutum dubu 1 da 777, sannan cutar ta kama mutum dubu 148 da 296. Sai dai tuni Nijeriyar an sayi allurar riga-kafin Korona na doz miliyan 1.4 daga kanfanin  AstraZenec wanda za a bayar da dubu 500 na farko a watan Fabarairun nan da muke ciki.

Ya zuwa yanzu a fadin duniya annobar korona ta yi ajalin mutum miliyan biyu da dubu dari hudu da ashirin da Tara da kuma dari takwas da ashirin da biyar, inda kuma mutum miliyan 110 da dubu 35 suka kamu da cutar a yayin da mutum miliyan 84 da dubu 865 suka warke daga cutar a doron kasa.

A cikin awanni 24 da suka gabata a kasar Indiya an samu karin rasuwar mutum 109 inda kuma mutum dubu 11 da 795 suka harbu da cutar. Kawo yanzu a kasar mutum miliyan 10 da dubu 937 da 320 sun kamu da cutar a kasar.


Post a Comment

0 Comments