GASAR ZAKARUN TURAI: PSG Ta Lallasa Barcelona Da Ci 4 Da 1

 

A ci gaba da gasar zakarun Turai zagaye na 16, kungiyar PSG dake Faransa ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ci 4 da 1. 

Wasan wanda aka buga shi a filin wasa na Camp Nou dake Sipaniya a cikin daren yau Talata, Barcelona ta fuskanci rashin nasara a dare na yau duk da kuwa Barcelona din ne ta fara zuwa kwallo a ragar PSG wanda Lionel Messi ya zura a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 27 da fara buga wasan. 

Sai dai a miniti na 32 Klyian Mbappe ya rama, inda wasan ya zama 1-1. Ana dawowa daga hutun rabin lokaci, Mbappe ya kara a minti na 65, inda a minti na 70 Moise Kean ya zura kwallo ta uku. 

A minti na 85 ne wasan ya koma 4 da 1 bayan da Klyian Mbappe ya kara. 


Post a Comment

0 Comments