RAHOTO NA MUSAMMAN: Gwamnatin Buhari Za Ta Cefanar Da Matatun Man Fetur Da Wadansu Kayayyakin Gwamnati

Shugaba Muhammadu Buhari
 

Daga Muhammad Farouk

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta shirya tsaf wajen cefanarwa da jinginar da kayayyakinta guda 36 a tsakanin watan Janairun 2021 har zuwa watan Nuwamban 2022. 

Gwamnatin Nijeriya za ta yi hakan ne domin samar da kudin da za ta gudanar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin 2021. 

Kayayyakin da gwamnatin za ta cefanar sun fito ne daga sashen hasken lantarki, masana’antu, sadarwa, gine-gine. Ana tunanin fara siyar da su daga watan Janairun 2021 zuwa watan Nuwamban 2022 kamar yadda majiyarmu ta PREMIUM TIMES ta labarto.

Takardar da majiyarmu ta gani gwamnati ce ta aika gaban majalisar kasa inda aka yiwa takardar take da; “NCP Approved 2021 Work Plan.” Inda aka nuna sunayen “ayyukan” da za a yi da kuma wuraren da za a cefanar da lokacin da za a dauka da kuma farashin kayayyakin. 

Majalisar kasa

Daga cikin manyan wuraren da gwamnatin za ta cefanar sun hada da Cibiyar kiyaye birnin Tarayya Abuja (Abuja Environmental Protection Board (AEPB), da Dakin taro na duniya dake Abuja (ICC), da wadansu matatun man fetur da ba a bayyana sunayensu ba, sai Kamfanin raba hasken wutar lantarki ta Nijeriya (TCN), sai Hukumar ruwa ta Abuja (Abuja Water Board), da kuma Cibiyar Fima-fimai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation) da sauran su. 

Matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cefanar da jinginar da wadannan wurare domin gudanar da ayyukan kasafin kudin Nijeriya na 2021 na naira Tiriliyan 13.58 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa kasafin hannu a ranar 31 ga watan Disambar 2020. 

Har wala yau gwamnatin ta fitar da tsare-tsaren yadda za a siyar da wadannan wurare, inda wadansu wuraren za a siyar da su ne baki daya, a yayin da wadansu za a cefanar da hannun jarin su ne, wasu kuma a jinginar da su. A yayin da wadansu za a maida su hannun ‘yan kasuwa baki daya. Ko a siyar da rabin hannun jarin. 

Wadansu wuraren da aka ware za a siyar an bada dama ga duk wadanda za su siya. 

Wadansu wuraren da aka shirya siyar da su za a nemi wanda zai siya ya biya kashi 51 domin ya zama mallakinsa, da kuma tsare-tsaren gudanar da wadannan wuraren, inda za a maishe da mallakar wurin daga hannun gwamnati zuwa hannun wanda ya siya. A cewar BPE (Bureau of Public Enterprise), an bada damar mai siya ya zama ko a daidaiku ko kuma kamfani, kuma zai iya zama dan Nijeriya ko daga kasar waje, da kuma kudin siya da na gudanar da kamfanin, da kayayyakin lura da tsare-tsaren da ake da bukata wajen tabbatar da cewa kamfanin zai samu riba. Dangane da wuraren da gwamnati ta shirya jinginarwa kuwa a tsarin da a Turance ake ce ma ‘Public-Private Partnership (PPP)’, inda gwamnati za ta ci gaba da rike rikon wurin, amma kamfanin da ya siya ne zai ci gaba da gudanar da wurin zuwa lokacin da aka kulla yarjejeniyar. 
Tsarin yadda wuraren yake da farashinsu

Dukkanin wuraren guda 36 an raba su zuwa gida biyar ne, kamar yadda takardar ta tabbatar, inda bangaren hasken lantarki ke da ayyuka tara, bangaren masana’antu da sadarwa ke da ayyuka takwas, da ci gaban wuraren, sai bangaren ma’adanan kasa ke da ayyuka shida. 

Sauran sun hada da gine-gine da kuma kulla alakar tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa inda ke da ayyuka hudu, sai bangaren ‘post transaction management’ ke da ayyuka tara. 

A kasa takaitaccen bayani ne na yadda ayyukan suke: Matsalar Da Aka Fara Fuskanta

Batun cefanar da wuraren da jinginar da su ya fara fita ga jama’a ne a yayin da BPE ta bayyana gaban majalisa domin kare kasafin kudin 2020 da ya gudana a watan Nuwamba. 

Duk da takardun da BPE ta mikawa kwamitin majalisar Dattawa dangane da maida wadansu wuraren hannun da ‘yan kasuwa  ya nuna gwamnatin tarayya ta shirya cefanar da Sashen hasken wutar lantarki na Geregu da Omotosho (Power Plants, Geregu, Omotosho) da kuma na Kalaba akan naira Biliyan 434 a shekarar 2021, da sauran su, sai dai kwamitin ya ce ba shi da masaniyyar cewa za a cefanar ko jinginar da wuraren. 

Shugaban kwamitin, Theodore Orji, ya ce kwamitin na su ba shi da masaniya kan batun, inda ya yi korafin cewa Babban Daraktan BPE din, Alex Okoh, “ya ki tafiya da membobin kwamitin.”


 Sai dai mako daya da batun, wannan kwamitin ya tabbatar da cewa wadansu daga cikin wuraren za a siyar da su a yayin da wadansu za a jinginar da su. Wannan ya biyo bayan ‘maslahar’ da aka samu tsakanin membobin kwamitin da kuma BPE din. 

Gwamnatin tarayyar har wala yau ita ma ta tabbatar da batun a lokacin da Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta gabatar da bayanai kan kasafin kudin ga masu ruwa da tsaki mako guda da wannan batun. 
Ta kara da cewa; wani karin bayani kan siyar da wadannan wuraren da kuma jinginar da wadansu wuraren na gwamnati shi ne; baya ga hakan, gwamnati har wala yau za ta ciwo bashi a cikin gida da waje a matsayin wata hanya na sake samun wadansu kudaden da za a yi ayyukan dake cikin wannan kasafin kudin. 

Daga cikin wuraren da tuni aka fara shirye-shiryen jinginar da su sun hada da; Tafawa Balewa Square, Kasuwar duniya ta Legas (Lagos International Trade Fair Complex), da kuma ‘Special Economic Zones’ dake Kalaba da Kano.

Adawa Da Batun Cefanar Da Wuraren Na Gwamnati 

Mutane da dama a daidaiku da kungiyoyi musamman na fararen hula sun soki matakin gwamnatin na siyar da wuraren kamar yadda suka soki matakin gwamnati na kara ciwo bashi. 

Adawa da wannan mataki na karshe, shi ne wanda kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Nijeriya ta yi. Inda kungiyar ta rubuta wata wasika zuwa ga majalisar kasa ta neman da majalisar ta dakatar da shugaban kasa daga siyar da wadannan wuraren, lamarin da ta ce na karya dokokin kundin tsarin mulkin kasar da kuma cin amana.SERAP ta ce a maimaikon a ci ba shi ko siyar da wuraren, akwai bukatar gwamnatin ta rage kudaden da take kashewa wajen gudanar da shugabanci musamman a rage albashi da alawus na ‘yan majalisun kasar, da kudaden da ake ba su wajen gudanar da ayyuka a yankunansu, da sauran su wanda hakan zai taimaka wajen samar da kudaden shiga. 

Da yake bayyana matakin gwamnatin na siyar da wadannan wuraren, SERAP ta ce hakan zai bada damar cin hanci da rashawa da kuma bayar da damar rashin gudanar da lamarin cikin tsari da daidaito, da kuma yi wa tsarin bayar da kwangila angulu da kan zabo, wanda ta ce hakan a nan gaba zai cutar da kasar. Inda ta bayyana hakan da cewa; ba zai taba amfanar da al’ummar kasar ba. 

Fassarar Wakilin Jaridar Madogara Da Madogara TV

Post a Comment

1 Comments

  1. In ya siyar a fada masa dan Allah Najeriyar ma ya sata a kasuwa ya siyar duk mu huta.

    ReplyDelete