Ranar Mukabala: Shaikh Abduljabbar Ya Aikewa Da Gwamna Ganduje Sabuwar Bukata

Daga Muhammad Farouk 

Shugaban Majamma’u Ashabil Kahfi Warraqeem, Dr Abduljabbar Nasiru Kabara ya sake mika sabuwar bukata ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano kan mukabalar da gwamnatin ta shirya gudanarwa a ranar 7 ga watan Maris din 2021 tsakaninsa da Malaman Kano a masarautar Kano. 

Shaikh Abduljabbar ya nemi hakan ne a wata wasika da ya sanyawa hannu kuma ya aikawa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda MADOGARA ta samu kwafinta, inda Shehin Malamin ya nuna farin cikinsa da jindadinsa bisa sanya ranar da gwamnati ta yi domin gudanar da mukabalar. Wanda ya ce tattaunawar zai bada damar fahimtar juna musamman idan aka yi adalci. 

Takardar da Shaikh Abduljabbar ya aikawa Gwamna Ganduje

Sai dai Shehin Malamin ya ce yana so a  bashi dama ya zo da littafansa da kuma jawabansa da ya gabatar tare da wani mutum daya da zai lura da littafansa da kuma daukar abubuwan da za a gabatar a cikin bidiyo da murya. 

Shaikh Abduljabbar ya ce ya dauki batun Manzon Allah da Sahabbansa managarta da muhimmancin gaske, inda ya ce: “ina mai sanar da mai girma gwamna cewa ban taba kuma ba zan taba darajar Manzon Allah ko Sahabbansa ba. Dukkanin karatukana da rubuce-rubucena na yi su ne wajen kare martaba da mutuncin Manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa da Sahabbansa managarta”, ya tabbatar. 

A karshe ya ce ya amsa goron gayyata kan wannan mukabalar, inda ya ce zai halarta da budaddiyar zuciya, inda ya ce yana fatan duk wadanda za su halarta za su je suma da budaddiyar zuciya. 

Takarda gayyata da gwamnatin Kano
ta mika Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara

A yau Lahadi ne Kwamishina mai kula da harkokin addini Dr. Baba Impossible a madadin gwamnatin jihar Kano ya gabatar da takardar gayyatar tattaunawa ga Sheikh  Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara da sauran wasu Malaman Addinin Musulunci a jihar Kano wanda aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi 7 ga watan Maris din 2021 a Fadar Masarautar Kano.

Daga hagu: Shaikh Abduljabbar Da Kwamishina
 mai kula da harkokin addini 
Muhammad Tahar (Baba Impossible)Post a Comment

0 Comments