'Rediyo Na Fuskantar Barazanar Gushewa Saboda Intanet'

 


Yau ce ranar Radiyo ta duniya. A shekara ta 2011 ne hukumar Kula da ilmi, da kimiyya da kuma al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta keɓe kowace ranar 13 ga watan Febrairu a zaman ranar yin waiwaye da zurfin tunani kan muhimmanci radiyo ga rayuwar al'ummar duniya.

A sakonta kan bikin na bana hukumar ta UNESCO ta yi kira ga tashohin radiyo da su yi bikin cikar shekaru goma da ƙirƙiro wannan ranar kana da cika shekaru 110 da samuwar radiyo a duniya.

Taken wannan shekarar shi ne "Sabuwar Duniya, Sabuwar Rediyo".

Alhaji Zaidu Bala shi ne shugaban Ƙungiyar Muryar Talaka da ke Najeriya kuma ya shaida wa BBC irin mahimmancin rediyo. A cewarsa, rediyo ce kafar yaɗa labarai da aka fi saurara.

Ya ce kusan kowa yana sauraron rediyo - "mu a wajenmu mun ɗauki rediyo kamar jami'a saboda wuri ne na ƙaro ilimi sosai".

Sai dai ya ce babban ƙalubalen da rediyo take fuskanta a halin yanzu, shi ne yadda komai ya koma kan intanet "yaran da za su taso a nan gaba ƙila wani ma zai daina ganin rediyo saboda harkar intanet da ta taso"

"Kowane gidan rediyo za ka ga ya buɗe shafin intanet yana watsa labarai kuma intanet ba kowane wuri ake samu ba - rediyo zamani zai sabuntar da ita amma idan aka yi wasa zamani zai rage mata shiga wasu wurare". in ji Zaidu Bala.

Ya ƙara da cewa suna ƙoƙarin ganin ana tafiya da zamani yadda mutane za su samu sauƙin kama tashoshin da ke kan gajere da kuma dogon zango ta wayoyinsu na salula.

-RAHOTON BBC HAUSA

Post a Comment

0 Comments