Rikicin Kabilanci Ya Barke Tsakanin Hausawa Da Yarbawa A Ibadan

Kasuwar Shasha inda rikicin ya balle

Daga Muhammad Farouk

Mutuwar wani baduku sakamakon caka masa wuka da wani dan dako ya yi ya janyo rikicin kabilanci a kasuwar Shasha dake garin Ibadan a jihar Oyo, lamarin da ya janyo kona dukiyoyi na miliyoyin nairori. 

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya labarto cewa; rikicin ya fara ne a ranar Alhamis, amma lamarin ya yi kamari ne a ranar Juma’a, a lokacin da aka tabbatar da mutuwar mai gyaran takalman sakamakon raunin da ya samu a yayin rikicin. 

Wani ganau ya shaidawa NAN  cewa dan dakon wanda yake Bahaushe ne daga Arewacin Nijeriya ya caka wa mai gyaran takalman wuka wanda yake shi kuma Bayarrabe ne sakamakon sabanin da suka samu a tsakaninsu. 

Ganau din ya ce nan take aka garzaka da shi zuwa asibiti domin yi masa magani, sai dai da safiyar ranar Juma’a aka tabbatar da rasuwarsa. Ya kara da cewa; hakan ya jefa ‘yan kasuwar cikin sabon rikici da kuma wadansu mazauna yankin, inda suka dira a kasuwar ta Shasha a ranar Juma’a domin daukar fansar kashe dan uwansu. 

Majiyarmu ta labartawa MADOGARA cewa; a yayin da ya kai ziyara a yankin da lamarin ya faru, ya tarar da yadda aka kone wadansu shaguna da kuma gidaje, inda ya tarar da kasuwar yashe ba kowa. 

Hukumomin tsaro ciki harda ‘yan sanda, gamayyar jami’an tsaron dakile miyagun laifuka da ake kira da ‘Operation Burst’ da kuma jami’an Amotekun sun kasance a wurare mabambanta a yankin domin dawo da zaman lafiya. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da faruwar lamarin a hirarsa da NAN a ranar Juma’a a Ibadan. 

Fadeyi ya ce rikicin ya fara ne sakamakon rashin jituwa da aka samu a tsakanin wanda aka kashe da wani kuma. 

“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ngozi Onadako, da kuma mai taimakawa gwamna Seyi Makinde sun je wurin sannan sun tattauna da bangarorin biyu,” inji Kakakin ‘yan sandan. 


Post a Comment

0 Comments