Sace Dalibai Mata a Zamfara: Sultan Da Tambuwal Sun Kai Ziyarar Jajantawa


Daga Husaini Ibrahim, Gusau

Kasa da awa goma sha biyu da sace dalibai Mata na Sakandire a Jangebe cikin karamar hukumar Talatar Mafara a cikin Jihar Zamfara, tawagar Sultan Sa'adu Abubukar da Gwamna Aminu Waziri Tanbuwal sun kai ziyar jajantawa al'ummar Jihar Zamfara da kasa baki daya

 A jawaban su, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da mai Martaba Sultan Sa'adu Abubukar sun bayyana kaduwar su da jin labarin sace dalibai Mata na Sakandire a Jangebe.

Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa wannan ba karamar masifa bace a kwashe Yara kanana a shiga daji da su kuma lallai wannan masifa ta shafi kowa ba ga iyayan daliban ya tsaya ba, inji gwamna Waziri Tambuwal.

Kuma ya tabbatar da cewa, za su dukufa wajan yin addu'oi domin ganin a ceto dalibai ba tare da wata ta rasa ranta ba inji gwamna Waziri Tambuwal.

A nasa jawabin takwaransa Gwamna Bello Matawalle Maradun, ya bayyana godiyarsa da zuwan tawagar Sultan Sa'adu Abubukar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal akan Jajantawarsu a lokacin da abin ya ke ciki zafin a zukatanmu.

Gwamna Bello Matawalle ya kuma tabbatar masu cewa, suna ta kokarin ganin yadda za su yi wajen ganin an ceto wadannan dalibai daga hannun miyagun ba tare da daya ta rasa ranta ba.

Post a Comment

0 Comments