Sanata Rochas Okorocha Ya Shiga Hannun 'Yan Sanda Bisa Yi Wa Motocin Gwamnati Rotse

A lokacin da 'yan sanda suka cafke
Sanata Rochas Okorocha
 Daga Muhammad Farouk 

Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo a yau Lahadi sun yi awon gaba da Sanata mai wakiltar Imo West a majalisar Tarayyar Nijeriya, Rochas Okorocha. 

Rochas Okorocha wanda yake tsohon gwamnan jihar ne, ‘yan sandan sun kama shi ne bisa zarginsa da tarwatsa kayayyakin gwamnati da kuma motocin jami’an tsaro tare da kuma shiga cikin ginin da gwamnati ta kwace na matarshi Nkechi. 

Kwamishinan fili na jihar, Enyinnaya Onuegbu a ranar Juma’a ya bayyana cewa gwamnati ta kwato ginin Royal Palm Estate dake titin Akachi a birnin Owerri wanda ake zargin na Nkechi ne.  Onuegbu ya ce gwamnati ta zagaye wurin har zuwa wani lokaci. 

Ya ce kwacen wurin na da alaka da shawarar da kwamitin bincike na jihar Imo ya bayar da ake kira da ‘Imo State gazette’ kan dawo wa da filayen gwamnati da wadansu kadarorin gwamnati. 

Ya ci gaba da cewa; “wannan yana daga cikin shawarwarin da kwamitin bincike ya bayar na yadda aka siyar filaye da wadansu kadarorin gwamnati ba bisa ka’aida ba a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2019, inda suka bayar da shawarar gwamnati na kwace irin wadannan wuraren,” inji shi. 

Kwamishinan ya ce wannan gwamnatin na iya bakin kokarinta wajen kwato kayayyakin da yake mallakin gwamnati ne amma aka sace su a gwamnatocin baya musamman wadanda aka sace a gwamnatin da ta gabata. 

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa; Sanata Rochas Okorocha a ranar Lahadi ya dira ginin da ake zargin na matarsa ne da gwamnati ta kwace, inda ya gargadi gwamnan jihar ta Imo Uzodinma da hukumomin tsaro akan su nesanci ginin. 

“daga zuwansa, ya nemi ya shiga muhallin, inda ya shaida wa jami’an tsaron da suke gadin wurin cewa babu wata umurni daga kotu da ta ce a killace wurin,” inji majiyarmu. 

“bisa wannan, ya jaddada bukatarsa na shiga muhallin, amma a karshe sai masu rakiyarsa suka karya makullin da aka rufe wurin. Daga nan ne aka fara harbe-harbe, a lokacin da wadansu mutum biyu mai taimakawa gwamna Uzodinma Chinasa Nwaneri da Eric Uwakwe, suka isa wurin da wadansu tawagar jami’an ‘yan sanda da matasa. Sai kuma ka fara cacar baki da harbe-harben kan mai Uwa da Wabi. Harsashi ya samu daya daga cikin ‘yan rakiyar Sanata Okorocha”, inji majiyarmu.

Ga wasu kadan daga cikin hotunan kamun da 'yan sanda suka yi masa da kuma rotsin da aka yi motocin 'yan sanda. 

Post a Comment

0 Comments