Sarkin Inyamurai Na Keffi Ya Koka Kan Yadda Ake Tsangwamarsu A Siyasar Nijeriya

 

Igwe Ohabuike Ohia Di Uru Eze Igbo Keffi IV
Daga Wakilinmu

Sabon mai sarautar Igwe Ohabuike Ohia Di Uru Eze Igbo Keffi IV a jihar Nasarawa, Chief Celestine C. Mbah ya nuna rashin jindadinsa bisa yadda ake nunawa Ibo bambanci a siyasar kasarnan. Inda ya ce; “an dade ana nuna wa Ibo bambanci a tsarin shugabanci da siyasar Nijeriya.”

Igwe din ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawar da Wakilinmu ya yi da shi, inda ya ce a taskace yake yadda Ibo suka taka muhimmiyar rawa wajen samun ‘yancin Nijeriya, wanda a cewarsa bai kamata a rika nuna musu bambanci ba a siyasar kasarnan.

 “abin da ibo ke gani a kasarnan, bama jin dadi. Muna kallon kanmu a matsayin wadansu mutane da aka yi watsi da su, kuma an sani cewa kafin a bai wa Nijeriya ‘yanci, muna gaba-gaba wajen ganin an samun ‘yancin kai”, ya koka.

Ya ci gaba d acewa; “mutanen irin su Nnamdi Azikwe ya yi amfani da jaridarsa ta African Pilot newspaper wajen gwagwarmayar samun ‘yanci, haka zalika Michael Okpara da sauran su, an yi saurin manta irin gudummawar da suka bayar wajen ‘yancnin Nijeriya”, ya tabbatar.

Cif Celestine har wala yau ya nemi gwamnati da ta rika adalci a lamuranta, domin rage yawan neman ta yi adalci daga mutane wanda koyaushe ke kara sanya kasarnan cikin matsala. Inda ya ce dole ne dama a  duk lokacin da ake nuna bambanci, mutane ba za su ji dadi ba.

Ya yi kira ga gwamnatin Nasarawa da su bai wa Ibon da suka dade a jihar damar taimakawa wajen kawo wa ci gaba ta hanyar sanya su cikin tsarin shugabanci a jihar. “wasun mu da dama mun dade, muna huldar kasuwanci, muna biyan haraji a nan, muna taimakawa wajen ci gaban jihar Nasarawa, a don haka jihar Nasarawa ya kamata ta sani, saboda wannan, su jawo mu a jika, ta bamu abin da ya dace damu”, ya lurantar.

Ya koka da cewa; “dukkanin ‘ya’yana a nan na haife su, ba su ma san gabashin kasarnan ba, amma idan ka zo batun ba da gurbin karatu, za a gaya musu cewa su ba ‘yan jihar bane”, inji shi.

“a don haka abin da muke cewa shi ne su rika bamu tamu damar a nan, idan ‘ya’yanmu suka kammala Sakandare, sai a ba su damar gurbin shiga jami’a a nan. Idan aka yi mana wannan, kowa zai ji dadi, kuma za a karfafa shi ya ci gaba da ayyukan da za su bunkasa ci gaban jihar baki daya”, inji Igwe Celestine.

Cif Celestine ya mika godiyarsa ga Sarkin Keffi, HRH Alh.  (Dr) Shehu Chindo Yamusa III bisa goyon bayan da yake bai wa Ibo, da sauran wadand aba ‘yan asalin garin Keffi bane, inda ya bayyana Sarkin a matsayin mutum mai son zaman lafiya da adalci, wanda yake taimakawa Ibo a kowanne lokaci. Inda ya ce Sarkin a kullum kira yake da a rika bin doka da oda musamman a duk lokacin da ya fuskanci akwai wata alama na rashin jituwa a masarautar. Ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da bai wa Sarkin ikon adalci da taimako a shugabancinsa.

A karshe ya yi kira ga Ibo da suke jihar Nasarawa da su zama masu bin doka da oda, tare da girmama hukumomi tare da sanya al’amuransu ga Allah. Inda ya ce an san Ibo da girmama ra’ayin jama’a da al’adunsu, inda ya ce ba za su sauya a hakan ba, inda ya bukaci su rika bin dukkanin ka’ida wajen bayyana damuwarsu idan an yi musu rashin adalci ta hanyar daukar matakai bisa doka.

 


Post a Comment

0 Comments