Satar Dalibai: Gwamnatin APC ta gaza -Hadimin Ganduje

Daga Wakilinmu 

Salihu Tanko Yakasai, wanda hadimin gwamnan Kano ne Dr Abdullahi Umar Ganduje kan kafofin yada labarai, ya ce gwamnatin APC ta gaza a wajen kare 'yan Nijeriya.

Yakasai ya wallafa hakan ne a shafinsa na twitter a ranar juma'a, don maida martani ga labarin sace dalibai mata na GGSS Jangebe da 'yan bindiga suka yi a jihar Zamfara.

"A matsayinmu na gwamnatin APC mun gaza, ta kowane mataki mun gaza cika alkawuranmu ga 'yan Najeriya, mun gaza kare rayuka da dukiyoyin al'ummar da suka zabe mu. Babu wata ranar da zata wuce ba tare da an samu matsalar tsaro a kasar nan ba. Wannan abun kunya ne ba kadan ba, idan ba zaka iya ba ka yi murabus," cewar Yakasai.

Sai dai a cikin jawabin da ya wallafa bai ambaci sunan wanda yake ikirarin ya yi murabus in har ba zai iya magance matsalar tsaro.

Hadimin gwamnan Kano, ko shekarar da ta wuce sai da gwamnan Kano Ganduje ya dakatar da shi kan kalamansa ga Buhari na gaza magance matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya, a lokacin zanga-zangar #SecureNorth.

Sai dai wannan martani nasa na zuwa ne, bayan sace daliban makarantar 'yan mata ta GGSS Jangele da wasu 'yan bindiga suka yi a daren ranar juma'a, a jihar Zamfara.

Post a Comment

0 Comments