Shugaba Buhari Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bawa A Matsayin Shugaban EFCC

 

Abdulrasheed Bawa

Daga Muhammad Farouk

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da sunan Abdulrasheed Bawa tare da aika sunan na shi ga Majalisar Dattawan Nijeriya domin tabbatar da shi a matsayin shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC.

A wata takarda da shugaban kasar ya aikawa shugaban majalisar Dattawan, Ahmad Ibrahim Lawan, shugaban ya ce ya yi hakan ne duba da sashen doka na 2(3) na 1, CAP E1 na dokar EFCC Act 2004 kamar yadda Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya tabbatar a sanarwar da ya fitar a yau Talata 16 ga watan Fabarairun 2021.

Bawa, mai shekara 40 a duniya, ya kasance kwararre ne wajen bincike sannan yana da basira a harkar abin da ya shafi binciken almundahana, rashawa, cin hancin jami’an gwamnati, halasta haramtattun kudi da sauran miyagun laifuka da suka shafi tattalin arziki.

Femi Adesina ya ce; Bawa ya samu horo na musamman a sassan duniya daban-daban, kuma yana daga cikin ma’aikatan EFCC na farko a 2005.

Bawa yana da digirinsa na farko a bangaren tattalin arziki, inda ya kuma ya yi digirinsa na biyu a bangaren huldar Jakadanci da diflomasiyya.

 

Post a Comment

1 Comments

  1. Allah ya sa zai iya aikin ba tsoro ba sonki. In almundahana ta koma ta na'ura zamani yan zamani ya kamata su yi bincike. Hausawa na cewa "karen bana shike maganin zomon bana"

    ReplyDelete