Sojojin Nijeriya Sun ‘Ƙwace Gonar Shekau’ A Dajin Sambisa

 

Sojojin Najeriya da ke yaƙi da Boko Haram a yankin arewa maso gabashi sun mamaye wata gona da suke ce ta Abubakar Shekau ce a dajin Sambisa.

Wani bidiyo da jaridar PRNigeria ta ce ta samu ya nuna yadda sojojin suka abka wa gonar da wasu kamar fararen hula suna kwasar amfanin gona.

A cikin bidiyon an ji sojojin na harbin bindiga suna yi wa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau shaguɓe cewa ya fito daga inda yake ɓuya.

“Shekau ina kake sarkin ɓaɓatu, ga mu a gonarka za mu yi sallar Juma’a a cikin Sambisa.”

“Ba ka ce za ka yi shahada ba, ka fito mu barar da kai.”

Jaridar PRNigeria ta ce sojojin bayan sun murƙushe wani hari a Dikwa sun kuma kama wasu masu taimakawa ƙungiyar ISWAP da bayanai.

Post a Comment

0 Comments