Sunayen Wadanda Suka Mutu Sakamakon Hatsarin Jirgin Saman Soji A Abuja


Jirgin saman dai ya kama hanyar zuwa Minna ne babban birnin jihar Neja, inda ya fuskanci matsalar injin lamarin da ya sanya shi mummunan hatsari da ya ci rayukan wadanda ke cikin jirgin. 

Majiyarmu ta Madogara ta labarto mana cewa; jirgin mai lamba Beechcraft KingAir B350i ya tashi ne a yau Lahadi kuma ya samu hatsari ne a daidai jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport dake Abuja

Ministan sufurin jirgin sama, Hadi Sirika a sakon da ya wallafa a Twitter ya ce; hatsarin mummuna ne. Ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa ransu. 

Ya zuwa yanzu majiyarmu ta fitar da sunayen mutum biyar cikin bakwai da suka rasu sakamakon hatsarin. 

Sunayen sune kamar haka: 

1. Flt. Lt. Gazama

2. Flt. Lt. Piyo

3. Flg. Offr. Okpara

4. FS Olawumi 

5. ACM Johnson.

Post a Comment

0 Comments