Tashin Bama-bamai A Jihar Borno Ya Kashe Mutum 10


Harin da Boko Haram suka kai a ranar Talata a babban birnin Maiduguri ta jihar Borno ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutum 10 tare da raunata fiye da mutum 21 sakamakon jefo rokoki da Boko Haram din ta yi. 

Boko Haram din sun jefo abubuwa masu fashewa har guda biyu cikin birnin na Maiduguri, inda ya dira a Adamkolo da Gwange. 

A hirar da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP suka yi da daya daga cikin jagororin Boko Haram din, Babakura Kolo ya ce; “mun kashe mutum shida a Adamkolo, hudu a Gwange daga harin bom din da muka kai”, ya tabbatar. 

Boko Haram din sun harbor bama-baman masu tashi ne daga Kaleri dake wajen birnin. Rahotanni sun nuna cewa an jikkata mutum 16 a Gwange, yayin da aka jikkata biyar kuma a Adamkolo, kamar yadda wani dan Boko Haram din, Umar Ari ya tabbatar. 

Wani ganau mai suna ama’ila Ibrahim ya ce; harin na Boko Haram ya firgita mutanen Maiduguri, saboda ba ya ga harin bom din, an bude wuta kan mai uwa da wabi. Sai dai ya ce cikin ikon Allah harbe-harben da aka yi bai sami kowa ba, amma sun kammala suka wuce zuwa Boboshe. 

Ibrahim ya ce ‘yan Boko Haram din sun fito ne ta kauyen Boboshe, wani fitaccen maboyar ‘yan Boko Haram din. 


Post a Comment

0 Comments