Tor Tiv Zai Shugabanci Kungiyar Sarakunan Kiristoci Na Nijeriya

 

Farfesa Orcivirigh James Ortese Iorzua Ayatse

Daga Zainab Muhammad

Sarakunan gargajiya a karkashin kungiyarsu ta Sarakunan gargajiya Kiristoci ta Nijeriya (AOCTRON) sun yi zama a Abuja domin tattauna batutuwan da suka shafi kungiyarsu domin kawo gyara da dora kungiyar akan bigiren kawo ci gaba ga al’ummarsu bisa manufofin kungiyar.

Sun ayyana amintattaun membobi goma a karkashin jagorancin Tor Tiv kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Binuwe, Mai martaba Farfesa Orcivirigh James Ortese Iorzua Ayatse, inda zai shugabanci kungiyar sannan ya jagoranci kwamitin amintattun kungiyar a lokaci guda.

Kwamitin amintattun AOCTRON sun yi wata sabuwar kwaskwarima, inda suka ayyana sabbin shugabancin a cikin kwamitin gudanarwa ta kasa inda aka zabi shugabannin kungiyar daga Arewa da Kudancin Nijeirya a matsayin wadanda za su rike mukamin mataimaka shugabancin kungiyar inda aka zabi Mai martaba Dr Da Jacob Gyang Buba, Gbong Gwon Jos kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Filato a matsayin mataimaki daga Arewa.

A bangaren kudancin kasar, aka zabi mai martaba Sarki Dandeson Douglas Jaja, Amanyanabo na Opobo kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Ribas.

Mataimakan shugabancin kungiyar guda biyu, daya daga kudanci daya daga arewaci an mika musu ragamar farfado da yankunansu domin kawo ci gaba mai amfani.

Har wala yau kwamitin amintattun ya yi duba ya zuwa ga halin da Nijeriya ta tsinci kanta na matsalar rashin tsaro, inda suka cimma shawarar shirya addu’o’i na musamman a fadin kasar tare da hadin guiwar Sarakunan gargajiya Musulmi.

Kwamitin wanda Farfesa Orcivirigh James Ortese Iorzua Ayatse, Tor Tiv ke yiwa jagoranci, har wala yau sun kai wa Sarkin Muslmi, kuma shugaban majalisar Sarakunan Nijeriya, Alhaji Abubakar Sa’ad ziyara, inda suka tattauna da shi tare da bayyana masa manufarsu na shirya addu’o’in saboda halin da Nijeriya ta tsinci kanta.


Post a Comment

0 Comments