Tsagerun Neja Delta Sun Yi Barazanar Kai Hare-hare A Abuja Da Legas

 

Tsagerun Neja Delta

Daga Muhammad Farouk

Wata kungiyar Tsagerun Neja Delta mai suna ‘Supreme Egbesu Liberation Fighters,’ sun yi barazanar tarwatsa manyan gine-gine a Legas da Abuja.

Kungiyar sun yi wannan barazanar ne a wani bidiyo da gidan Talabijin na AIT ya saki a ranar Talata. Inda a cikin bidiyon, kungiyar suka zargi gwamnatin Nijeriya da nuna musu tsangwama da wariya a yankin na su, inda suka ce gwamnatin ta gaza wajen kaddamar da shirin nan na afuwa zuwa gare su.

Da yake karanta sanarwar barazanar, wani mutum da ya rufe fuskarsa, ya ce babu wani takamaimen ci gaba da aka kawo a yankin tun bayan amincewarsu da shirin afuwa da gwamnatin tarayya ta yi.

 “har zuwa yau, babu wadansu ingantattun makarantu, babu ruwan sha mai kyau, babu hasken wutar lantarki, babu asibitoci, babu hanyoyi masu kyau ga al’ummarmu domin su amfana,” inji mutumin da ya rufe fuskarsa.

Har wala yau, a cewar kungiyar, ba za a iya nuna wani takamaimen ci gaba da za a ce an kawo kan batun aikin share Ogoni ba, shirin da aka fi sani a turance da ‘Ogoni clean-up project’.

Inda kungiyar ta ce gwamnatin tarayya sai ta zabi ta yi siyasa kan wadannan ayyukan ci gaban da ta yi wa al’ummarsu alkawari. Sun kara da cewa; “yadda aka bar al’ummar Zamfara suna lura da arzikin zinarensu, mu ma al’ummar Neja Delta a bar mu mu kula da arzikin da muke da shi”, inji su.

Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda ake yi wa al’ummar su a yankin Neja Delta, inda gwamnatin Nijeriya ta kasa samar wa da al’ummarsu ingantaccen muhalli da kayan more rayuwa a tsawon shekaru.

“abin da kawai muke gani shi ne tarin sojoji a jiragen ruwa da dimbin jami’an soji da aka barbaza su a yankin Neja Delta, wadanda ba abin da suke yi sai kashe mu, zaluntarmu wadanda ba su ji ba su kuma gani ba, yiwa matanmu fyade, da sauran su”, suka tabbatar.

Kungiyar ta ci gaba da cewa; a koyaushe gwamnatin tarayya ta sanya matakan tsaro iri-iri na sirri, wadanda wadannan hukumomin tsaro koyaushe suna cutar da al’ummarsu. “ku duba ku ga yadda yanzu yankinmu da yake da ruwa sosai, an dauko Kamfanin Isra’ila na aikin samar da tsaron ruwan wanda ma mu mun fi so kwarewa da sanin yadda ake samar da tsaro ta ruwan”, suka lurantar.  

Sun kara da cewa; “ka da ku damu, muna nan tafe domin tarwatsa dukkanin wadansu gine-gine a Abuja da Legas. A matsayinmu na kungiyar da ke son kwatar ‘yancin al’ummarmu, zamu tarwatsa dukkanin bututun man fetur nan bada jimawa ba. Sai mun durkusar da tattalin arzikin Nijeriya”, suka tabbatar.

Kungiyar sun ayyana tsohon shugaban kasar Nijeriya, Goodluck Jonathan da kuma Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a matsayin wadanda za su jagorance su wajen sulhu da gwamnatin Nijeriya.

 


Post a Comment

0 Comments