Tsohon Shugaban Kare Hakkin ‘Yan Jarida Ta Afrika Farfesa Gwarzo Ya Yi Alhinin Rasuwar Dan Jaridar VOA Abdulaziz

 

Marigayi Ibrahim Abdulaziz (VOA)


Tsohon Shugaban Kare Hakkin ‘Yan Jarida Ta Afrika Farfesa Gwarzo Ya Yi Alhinin Rasuwar Dan Jaridar VOA Abdulaziz

Tsohon shugaban kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta Afrika, RPJA, Farfesa Gwarzo ya yi alhinin rasuwar Dan Jaridar gidan rediyon muryar Amurka, VOA, Ibrahim Abdulaziz. Farfesa Gwarzo ya bayyana rasuwar dan jaridar a matsayin babban rashi da kungiyar ta yi, inda ta ce memba shi jajirtacce. 

Ibrahim Abdulaziz ya rasu ne a ranar 6 ga watan Fabarairun 2021 sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru da shi a hanyar zuwa Bauchi daurin aure. Ya rasu yana da shekara 49 a duniya. 

Tsohon shugaban kungiyar PRJA din, kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN) ya bayyana kaduwarsa da alhininsa ne a cikin sakon ta’aziyyarsa da ya sanyawa daga birnin Paris kuma ya aikawa manema labarai a Kano a ranar Juma’a.

A cewar Farfesa Gwarzo, mutuwar Ibrahim Abdulaziz Yola kuma memba a kungiyar PRJA babban rashi ne, ba kawai ga iyalinsa ba, harma da kunfgiyar PRJA da kuma aikin jarida baki daya. 

Kwamared Adamu Gwarzo ya ce ya yi aiki da Marigayi Abdulaziz a lokacin da yake jagorancin kungiyar PRJA, inda shi kuma Marigayin yake a matsayin wakilin kungiyar a arewa maso gabashin Nijeriya. 

“na san yadda yake da jajircewa da sadaukarwa wajen ganin ‘yan jarida sun yi aikinsu ba tare da an take musu hakkin na su ba. Bayan mun yi aiki da shi a kungiyar, mun kuma yi aiki da shi a VOA, inda yake aiki a sashen Hausa Ni (Adamu Gwarzo) nake aiki a sashen Faransanci. Dan jarida ne mara tsoro wanda yake aikinsa bisa gaskiya da rikon amana,” inji Adamu Gwarzo.

A karshe ya yi addu’ar Allah ta’ala ya jikan mamacin, ya kuma yafe kurakuransa, yasa aljannah Firdausi ce makoma. Sannan ya yi addu’ar Allah ya bai wa iyalinsa da ‘yan’uwansa da ‘yan’uwa da abokan arziki da abokan aiki hakurin jure rashinsa. 

Marigayin ya rasu ya bar mata uku tare da ‘ya’ya Tara, kuma tuni aka bizne shi a garinsu Yola dake jihar Adamawa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.


Post a Comment

0 Comments