Wanda Ya Saci Daliban Kankara Ya Mika Wuya A Zamfara

Auwalun Daudawa

Daga Muhammad Farouk 

Wani jagoran daya daga cikin kungiyoyin ‘Yan Fashin daji da ya dade ya na barna a shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya ya ajiye makamansa a karkashin wata yarjejeniya da Gwamnatin jihar Zamfara karkashin gwamna Bello Muhammad Matawalle.

Auwalun Daudawa ya kasance shi ne ya jagoranci sace daliban makarantar Sakandaren Kankara dake jihar Katsina a cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Gwamnan jihar Zamfara na ganin sulhu a matsayin abin da ka iya kawo zaman lafiya daga matsalolin tsaro da yake addabar jihar. Sai dai masana harkokin tsaro na ganin hakan a matsayin karfafa ‘yan ta’adda. Inda suka jaddada cewa dole ne a rika hukumar wadanda suke da hannu wajen ta’addanci a kasarnan. 

Hukumomin a Nijeriya a gefe guda kuma na ci gaba da gudanar da bincike don tattance wasu daga cikin kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma ke haifar da tashin hankali a Nijeriya wacce take fuskantar wadannan matsalolli tsawon shekaru.


Post a Comment

0 Comments